Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ita ce hukuma mafi ƙarfi a faɗin ƙasar, ta fuskar yaƙi da cin hancin.
Gwamnan ya tabbatar da haka ne, kan ƙoƙarin hukumar na yaƙi da cin hanci tare da tabbatar gaskiya da kyakkyawan shugabanci a jihar.
Wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar a ranar Talata, ta ce Ganduje ya faɗi haka ne a lokacin wani taron ƙungiyar Akantocin Nijeriya ANAN, mai taken taswirar samar da kyakkyawan shugabanci.
