Home Labarai Mun gaji da zaman gida haka nan – Ɗaliban Nijeriya sun koka

Mun gaji da zaman gida haka nan – Ɗaliban Nijeriya sun koka

54
0

Kungiyar dalibai ta Nijeriya NANS ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i su dawo da ayukkan jami’o’in gwamnati.

Kungiyar Daliban ta kuma umurci dukkan rassanta na manyan makarantun kasar, su kafa kwamitin tabbatar da bin ka’idojin kariya da cutar Covid-19 da za a kafa a lokacin bude jami’o’in.

Shugaban kungiyar Sunday Asefon ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

A ranar Litinin ne dai kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Covid-19 ya ce ba lallai a bude makarantun ba a ranar 18 ga wata.

Saidai kungiyar NANS ta ce a maimakon dage lokacin sake bude makarantun, zai fi dacewa a magance yaduwar cutar da ake ci gaba da samu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply