Home Labarai Mun gama lamuntar raini daga mataimakan Buhari – Ahmad Lawan

Mun gama lamuntar raini daga mataimakan Buhari – Ahmad Lawan

207
0

Shugaban majalisar Dattawan Nijeriya Ahmad Lawan ya ce majalisar ƙasar ba za ta ci gaba da lamuntar rashin girmamawar da mataimakan shugaba Muhammadu Buhari ke yi masu ba.

Lawan ya faɗi haka ne a ranar Litinin, lokacin da yake ganawa da ƴan jaridar fadar shugaban ƙasa, bayan Buhari ya ƙaddamar da kwamitin tuntuɓa tsakanin ɓangaren zartaswa da na majalisa wanda mataimakin shugaban ƙasar Yemi Osinmajo zai jagoranta.

Lawan wanda ya yi wannan maganar kan wasu daga cikin mataimakan shugaban ƙasar da ke yi wa majalisar kallon hadarin kaji, ya ce an kafa kwamitin ne domin inganta harkokin mulki tsakanin ɓangarorin biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply