Home Labarai Mun kashe ₦1.56bn don inganta rayuwar talakawan Kebbi – Sadiya Faruƙ

Mun kashe ₦1.56bn don inganta rayuwar talakawan Kebbi – Sadiya Faruƙ

67
0

Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe Naira ɗaya da miliyan 56 da dubu 200 kan shirye-shiryen tallafawa jama’a, a jihar Kebbi kaɗai.

Ministar bada agaji, hana faruwar ibtila’i da tallafawa jama’a Hajiya Sadiya Umar Faruƙ ta bayyana haka a lokacin ƙaddamar da wani shirin tallafawa matan karkara da ya gudana a masaukin shugaban ƙasa da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis, inda sama da mata dubu biyar suka samu tallafin Naira 20,000 kowaccensu.

 

Hajiya Sadiya Umar Faruƙ, ta ce gwamnatin tarayya ta fito da shirye-shirye daban daban domin inganta rayuwar jama’ar ƙasar tun a shekarar 2016.

Ministar ta ce maƙasudin ɓullo da shirin tallafin, don matan su samu abun yi da za su dogara da kan su kuma tattalin arziƙin ƙasa ya bunƙasa.

 

Haka kuma ta yi kira ga matan su sama da dubu biyar, su yi amfani da tallafin kuɗin na Naira 20,000 da kowaccensu ta samu, ta hanyar da za ta amfane su kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu dangane da manufar ƙirƙiro da shirin tallafin.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, wanda Sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Babale Umar Yauri ya wakilta, ya bayyana jin daɗinsa dangane da irin shirye-shiryen tallafawa jama’a da gwamnatin tarayya ke yi tun farkon zuwanta.

 

Wasu daga cikin matan da suka amfana da tallafin sun bayyana jin daɗinsu tare da bada tabbacin za su yi amfani da kuɗin wajen inganta rayuwarsu.

Shirye-shirye da dama ne dai gwamnatin tarayya ta ɓullo da su domin rage raɗaɗin talauci da kuma bunƙasa tattalin arziƙi, tun bayan da ƙasar ta faɗa rikicin tattalin arziƙi a shekarar 2016.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply