Home Labarai Mun kulle Kaduna ne don shiryawa coronavirus – El-Rufa’i

Mun kulle Kaduna ne don shiryawa coronavirus – El-Rufa’i

110
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta samar da gadaje 20 zuwa 30 ga manyan asibitocin jihar da ke da isasshen wuri domin kula da masu kamuwa da cutuka masu yaduwa.

Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya bayyana haka a Kaduna, lokacin da yake magana kan matakan da jihar ke dauka na yaki da cutar Covid-19 a jihar.

Gwamnan ya fadi hakan ne a bayanin da ya yi ta kafofin yada labaran jihar a ranar Laraba.

A cewar sa, kulle jihar da aka yi, ya ba gwamnati damar daukar matakan ko ta kwana a bangaren kiwon lafiya da kuma kare yaduwar cutar tun a farkon lokaci.

El-Rufa’i ya kuma bada tabbacin cewa nan da ‘yan kwanaki za samar da gadaje 70 a cibiyoyi biyu da ke fadin jihar a daidai lokacin da jihar ta mayar da wasu otal biyu a matsayin wuraren kebance jama’a.

Ya kara da cewa gwamnatin sa na gina wata cibiyar kula da masu cutuka masu yaduwa, mai cin gadaje 136, waddda ake sa ran za a kammala ta a karshen watan nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply