Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta kwato fiye da kadada 500,000 na gonakin noma a cikin shekaru uku da suka gabata, sakamakon inganta matakan tsaro da suka ba manoma damar komawa gonakinsu.
Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron cin abinci na musamman da Kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano ta shirya a matsayin wani bangare na taron bitar da take gudanarwa duk shekara a Kaduna.
Ya ce tsarin da gwamnati ta bi wajen yaki da matsalar rashin tsaro ya haifar da sakamako mai kyau a fannoni daban-daban.
Maiyaki ya bayyana cewa a baya ’yan bindiga sun mamaye wasu al’ummomin karkara, inda suke karbar haraji, tsara yadda za a yi noma, har ma da karbar kudin sadaki.
Ya ce: “Lamarin ya yi tsanani har manoma ba sa iya zuwa gonakinsu. Amma a yau, sakamakon tsaron da al’umma ke jagoranta da kuma tsarin gargadin gaggawa, zaman lafiya ya dawo, kuma manomanmu sun koma gonakinsu.”
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta hada matakan soji da sauran hanyoyin da ba na soja ba, ta hanyar bai wa sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki damar taka muhimmiyar rawa wajen yaki da rashin tsaro.
Maiyaki ya ce tsakanin shekarar 2023 zuwa farkon shekarar 2026, an gano rikici guda 75, inda aka yi nasarar magance guda 70, lamarin da ya taimaka wajen hana barkewar rikice-rikicen kabilanci da na addini.
Kwamishinan ya ce inganta tsaro ya kuma bai wa gwamnati damar kara zuba jari a harkar noma, inda kasafin kudin bangaren ya karu daga naira biliyan 1.4 a shekarar 2023 zuwa sama da naira biliyan 100 a shekarar 2026.
A cewarsa, karin jarin da aka zuba ya taimaka wajen rabawa manoma takin zamani kyauta, lamarin da ya kara yawan amfanin gona daga buhu uku a kowace hekta zuwa buhu 22 na masara.
Ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali kan sakamako da shirye-shiryenta ke samarwa maimakon yadda ake aiwatar da su kawai, domin rage karancin abinci da dawo da martabar al’ummomin karkara.
Maiyaki ya kuma yi bayani kan ayyukan more rayuwa da ake gudanarwa a kananan hukumomi 12, inda ya ce gina wa da gyaran hanyoyi ya rage lokacin tafiya, ya rage asarar amfanin gona bayan girbi, tare da inganta aikin kai daukin gaggawa.
Ya bayyana cewa ingantattun hanyoyi sun bai wa manoma damar kai amfanin gonakinsu kasuwanni cikin sauki, sun taimaka wa yara wajen zuwa makaranta, sannan sun bai wa jami’an tsaro damar mayar da martani cikin sauri idan aka samu kiran neman agaji.
