Home Labarai Mun sace yaran Ƙanƙara don nuna wa Masari iyakarsa – Auwalun Daudawa

Mun sace yaran Ƙanƙara don nuna wa Masari iyakarsa – Auwalun Daudawa

69
0

Auwalun Daudawa, mutumin da ake kyautata zaton ya kutsa satar daliban sakandaren Kankara jihar Katsina, yace ya jagoranci sace wadannan dalibai ne domin nuna wa gwamna Aminu Masari cewa karansu ya isa tsaiko.

A cikin wata ganawa da Daily Trust, Awwalun Daudawa yace yana so ne ya nuna wa gwamna Masari cewa yana karfin ikon aikata wannan aika-aikar.

Yace gwamna Masari ya rigaya yace ba zai sake sasanci da wasu ‘yan bindiga ba, ta haka ne ya ga ya kamata ya nuna wa gwamna Masari cewa zai iya aiwatar da wannan aikin.

Awwalun Daudawa yace bai taba aiwatar da irin wannan aikin a wata jiha ba, sai Katsina, ita ma don nuna wa gwamnatin cewa mutanensa nada karfi.

DCL Hausa ta gano cewa kafin dai Awwalun Daudawa ya ajiye makamansa ya rungumi sulhun gwamnatin jihar Zamfara, shi ne babban dakaren a sansaninsa da ke Dajin Dumburum cikin karamar hukumar Zurmi jihar Zamfara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply