Home Labarai Mun samu nasara ga tsarin mu na hana shigo da abinci –...

Mun samu nasara ga tsarin mu na hana shigo da abinci – Buhari

74
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayanin cewa ya dakatar da babban bankin Nijeriya CBN daga bada canjin kudi kasar waje ga masu shigo da kayan abinci ne domin tabbatar da kasar na samar da wadataccin abinci da kan ta.

Shugaban kasar ya ce wannan yinkuri ya haifar da da mai ido, domin kuwa ya sa kasar ta rage miliyoyin daloli da ake kashewa wajen shigo da abinci daga kasashen waje.

Da yake magana a lokacin da ya karbi wakilan Concil for New Nigeria Intiative (CNNI) da suka kai masa ziyara a fadar sa da ke Abuja a jiya Juma’a karkashin jagorancin Sanata Abu Ibrahim, Buhari ya ce wajibi ne kasar ta zuba jari a bangaren noma, kasancewar sa tushen arziki.

A cewar Buhari, “Duba da yawan mutanen da muke da shi da fadin kasa, noma ne abun da ya kamace mu. Mun gwada kuma mun gani, lokacin da muka zo a 2015. Mun karfafawa jama’a gwiwa su koma gona, kuma Allah ya albarkace mu da damina uku zuwa hudu masu albarka a jere. Kuma mun shaida cewa wadanda suka koma noman sun ji dadin sa,” a cewar Buhari.

Shugaban kasar ya kuma yabawa ‘yan kungiyar ta CNNI wadanda suka sadaukar da kan su wajen ciyar da kasa gaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply