Home Sabon Labari Mun shirya tsab don sake maka Kalu Kotu – EFCC

Mun shirya tsab don sake maka Kalu Kotu – EFCC

122
0

Hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC ta ce a shirye take ta fara shari’ar tsohon gwamna Orji Kalu nan take.

Hukumar ta fadi haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta Dele Oyewale ya fitar a yau, inda yake magana kan hukuncin da kotun koli ta yanke a yau.

Kotun kolin dai ta soke hukuncin da aka yankewa Kalu tare da bada umarnin a gudanar da sabuwar shari’a tana mai cewa Alkali Muhammad Idris bai da hurumin sauraron shari’ar Kalu domin an mayar da shi kotun daukaka kara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply