Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Mun yi babban tanadi ga manoman bana – Gwamnatin Kebbi

Mun yi babban tanadi ga manoman bana – Gwamnatin Kebbi

123
0

Gwamnatin jihar Kebbi ta jaddada ƙudirin ta na inganta harkar noman daminar bana a jihar.

Gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu ne ya sanar da hakan a wani taron tattaunawa da hukumomin aikin gona dake jihar.

Taron tattaunawar ya mayar da hankali ne kan yadda za a taimakawa manoma da kayan aiki da suke bukata yayin noman.

A zantawa sa da manema labarai kwamishinan gona na jihar Barista Attahiru Maccido ne ya sanar da hakan bayan kammala tattaunawar.

Taron tattaunawar dai ya samu halartar dukkanin masu ruwa da tsaki akan harakar noma dake jihar ta Kebbi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply