Home Labarai Mun yi gwanjon motocin da muka kwato ne ga fadar shugaban kasa...

Mun yi gwanjon motocin da muka kwato ne ga fadar shugaban kasa – Magu

212
0

Dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC Ibrahim Magu ya ce wasu daga cikin ababen hawan da hukumar ta kwato an yi gwanjonsu ne ga fadar shugaban kasa, ma’aikatar agaji da kyautata rayuwar jama’a da kuma hukumar tattara kudaden shiga.

Ya kara da cewa har yanzu wasu hukumomin ba su biya kudaden ba, saidai akwai yarjejeniya za a rika cire kudin daga kason kudaden da ake ware masu.

A cikin wata takarda da ya aike wa kwamitin Alkali Ayo Salami da ke bincikensa, Magu ya yi bayanin yadda aka yi gwanjon motocin.

Wannann takarda dai na matsayi maida ba’asi kan rahoton binciken dukiyar da aka kwato, wadda kwamitin ke zargin Magu da kin mayar da kudin da suka hau, da suka kai naira Biliyan 550 da kuma wasu gidaje da motoci.

Saidai wasu rahotanni sun ce yinkurin Lauyan Magu, Wahab Shittu na mika takardar ga kwamitin a ranar Litinin bai samu karbuwa ba, inda kwamitin ya nuna babu bukatar sai ya karbi takardar, domin zai iya sake gayyatar Magun idan akwai bukatar wani karin bayani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply