DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeLabaraiMun yi mamaki da har yanzu jami'an tsaro ba su yi wani...

Mun yi mamaki da har yanzu jami’an tsaro ba su yi wani abu ba kan kwamishinan Borno da aka yi zargin ya yi barazanar guntule yatsun duk wanda bai zabi APC ba – Amnesty International

Kungiyar Amnesty International ta nuna matukar damuwa kan yadda har yanzu hukumomin tsaro ba su dauki wani mataki kan Kwamishinan wasanni da ci gaban matasa na Jihar Borno ba, Sainna Buba, duk da hujjojin da ke akwai a fili kan kalaman da ya yi a wani gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar a Maiduguri a ranar 29 ga Agusta.

Amnesty International ta ce barazanar da Kwamishina Sainna Buba ya yi cewa za a “yanke yatsu” ga mutanen da ba za su kada kuri’a ga APC ba, bai kamata a daukarta a matsayin salon magana ko misali ba.

Kungiyar ta bayyana kalaman a matsayin barazana kai tsaye, kuma ta ce ya kamata Kwamishinan ya fuskanci hukunci kan abin da Amnesty ta kira yunkurin tunzura jama’a a boye.

Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta jaddada cewa hakkin dan Adam na al’ummar jihar Borno dole a mutunta shi tare da kare shi.

Ta kuma ce ya kamata kowa ya samu damar kada kuri’a cikin ’yanci, ba tare da wani mutum ko wata kungiya ta yi wani abu da zai tauye masa damar yin zabin siyasa ba.

Amnesty International ta na kira ga hukumomin tsaro su dauki matakin da ya dace kan kalaman Kwamishina Sainna Buba, domin tabbatar da cewa barazanar siyasa da kalaman da ka iya haddasa tashin hankali ba su zama hanyar hana jama’a gudanar da zabin da kundin tsarin mulki ya ba su ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata