Home Labarai Muna nan kan bakan mu, sai hafsoshin tsaro sun yi murabus –...

Muna nan kan bakan mu, sai hafsoshin tsaro sun yi murabus – Majalisar Wakilai

74
0

Majalisar wakilai ta Nijeriya ta ce tana nan kan bakan ta na lallai sai hafsoshin tsaron kasar sun yi murabus ko a sauke su, duk kuwa da ganawar da suka yi da hafsoshin tsaron a ‘yan kwanakin nan.

Hafsoshin tsaron Nijeriya

Mai Magana da yawun majalisar Benjamin Kalu ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau.

Ya ce idan dai har ba a gabatar da wani kudirin janye wannan matsaya ba, majalisar na nan kan bakan ta kan lallai sai an sauke hafsoshin ko su sauka.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Laraba 29 ga watan da ya gabata ne, majalisar wakilai ta bukaci hafsoshin tsaron su sauka ko a sauke su, saboda kasawar su wajen magance matsalar tsaron da ke addabar kasar.

Wannan ya biyo bayan wata doguwar mahawara da aka tafka kan kudirin da mai tsawatarwar majalisar Tahir Monguno (APC, Borno ya gabatar kan bukatar kawo karshen hare-haren Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

Kuma a wannan rana ne dai, majalisar ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari, ya umarci rundunar sojin sama da ta kasa, su kara tsananta bincike kan hanyoyin kasar musamman a yanken na Arewa maso Gabas da Yamma.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply