Home Kasashen Ketare Murna a Uganda bayan dawowar intanet

Murna a Uganda bayan dawowar intanet

45
0

Jama’ar Uganda na murnar dawowar sadarwar intanen a kasar bayan an rufe kafofin makon jiya, kafin fara zaben kasar.

Saidai har yanzu kafafen sada zumunta sun kasance a toshe inda ake yi shiga kafafen ta hanyar kafar sirri ta VPN.

Shugaba Yoweri Museveni wanda ya lashe zaben kasar karo na shida, ya zargi kafafen na Intanet da nuna son zuciya.

Saidai Dantakar shugaban kasar a jam’iyyar adawa ta NUP Bobi Wine, ya yi zargi tafka magu a zaben.

Kakakin jam’iyyar Joel Senyonyi ya zargi Museveni da rufe kafafen intanet ne domin hana jama’a yada hujjojin irin magudin da aka tafka a lokacin zaben.

Amma dai a ranar Asabar Shugaba Musaveni ya ce zaben da aka gudanar zai iya kasancewa zabe mafi inganci a tarihin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply