Hukumar zaben Uganda ta sanar da shuagba mai ci Yoweri Museveni a amtsayin wanda ya lashe zaben Uganda da aka gudanar a ranar Alhamis. Sakamakon zaben ya nuna Museveni ya samu kaso 58.6 na kuru’un da aka kada yayin da babban mai adawa da shi matashin mawaki Robert Kyagulanyi da ake wa lakabi da Bobi Wine ya samu kaso 34.8.
Sai dai tun kafin a fitar da sakamakon Bobi Wine yay i zargin an yi masa magudi kuma an bayar da rahoton jibge sojoji a gaban gidansa.
Labari mai alaka: Musaveni na kan gaba a zaɓen shugaban ƙasar Uganda
An hana amfani da kafafen intanet a Uganda
Uganda ta sa ranar zaben shugaban kasa
A lokacin gangamin yakin neman zabe Shugaba Museveni ya rinka bugun kirjin cewa a cikin shekaru 35 da ya kwashe yana mulkar Uganda ya yi wa matasa irinsu Bobi Wine riga-da wando; tun da ya samar musu da tsarin kiwon lafiya da ilimin da ya ba su damar kauce wa mutuwa daga cututtukan da ke addabar kananan yara. To amma matasan kasar wanda kafin zaben galibinsu suka nuna goyon bayansu ga matashin mawaki Bobi Wine na sukar Museveni saboda ya gaza samar musu da aikinyi.
