Home Labarai Mutane 17 sun mutu a wani hadarin mota

Mutane 17 sun mutu a wani hadarin mota

208
0

Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Nijeriya, (FRSC) ta ce wani hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar wasu matafiya su 17 a karamar hukumar Akwanga da ke jihar Nasarawa a daren Asabar.

Kwamandan hukumar ta “Road Safety” na garin Akwanga, Ebere Onyegbaduo ya ce, “Mun samu kiran waya a daren Asabar da aka sanar da mu wani mummunan hatsari da misalin karfe 7 na dare a titin Akwanga zuwa Gudi.

“Mun garzaya zuwa wurin da abin ya faru sai muka tarar da wata mota kirar Sharon VW da kuma wata Toyota Sienna na ci da wuta tare da mutanen da ke cikin motocin” inji Ebere.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply