Mutane 18 ne suka rasu bayan da jirgin kwale-kwale mai dauke da manoma 23 ya kife a jihar Bauchi.
Duk dai cewa mutane 5 sun tsira da ransu, amma dai rahotanni sun ce direban kwale-kwalen da wani mutum daya na can magashiyyan.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Ahmad Wakili ne ya sanar da hakan a cikin wata takarda da aka raba wa ‘yanjarida a Bauchi.
Takardar ta ce daga cikin wadanda suka rasu akwai yara 8 maza da ‘yan mata 8 sai manya guda 2.
Ya ce lamarin ya afku ne a kogin Buji na karamar hukumar Itas Gadau jihar Bauchi.
