Home Kasashen Ketare Mutane 3 sun mutu, 21 sun raunata a gobarar da ta tashi...

Mutane 3 sun mutu, 21 sun raunata a gobarar da ta tashi a gidan yarin Saudiyya

82
0

Da sanyin safiyar Alhamis ne wata gobara ta tashi a gidan yarin da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya, har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 3, da raunata 21, a cewar rahotanni.

Tuni dai an kwashe ‘yan gidan yarin an kuma garzaya da wadanda suka jikkata asibiti kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya ya sanar.

Rahotanni sun ce tuni dai jami’an kwana-kwana da tallafin wasu jami’an tsaro suka shawo kan gobarar.

Ba a dai bayyana dalilin tashin gobarar ba, amma dai hukumomi sun ce sun kaddamar da kwamitin bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.

Tashin gobara dai ya zamo ruwan-dare a kasar Saudiyya, wasu lokutta ana danganta hakan da karancin bin dokoki da ka’idojin sarrafa makamashi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply