Home Kasashen Ketare Mutane 3 sun mutu bayan arangama tsakanin lauyoyi da likitoci a asibiti

Mutane 3 sun mutu bayan arangama tsakanin lauyoyi da likitoci a asibiti

92
0

Kusan mutane 3 da ke da ciwon zuciya suka mutu bayan da rukunin lauyoyi suka kai hari ga likitoci a asibitin birnin Lahore na kasar Pakistan.

Rukunin lauyoyin sama da 200 da ke da matsala da likitocin ne suka fantsama cikin asibitin su na lalata kaya hade da ababen hawa. Jami’ai sun ce hatsaniyar ta samo asali ne biyo bayan wani guntun faifan bidiyo da aka nuna likitocin suna sukar lauyoyi.

Ministan watsa labaran Punjab Fayyaz-ul-Hassan wanda ya isa asibitin don shiga tsakani, shi ma lauyoyin sun hada da shi. Wata tashar talabijn mai zaman kanta ta nuna faifan bidiyon inda lauyoyi ke lalata kayayyakin a asibitin.

Firaiminista Imran Khan wanda ya ba da umurnin a gudanar da bincike kan lamarin, ya sha alwashin daukar kwakkwaran mataki kan duk wanda aka samu da laifi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply