Home Labarai Mutane 31,000 sun nemi aikin malanta 2,500 a Osun

Mutane 31,000 sun nemi aikin malanta 2,500 a Osun

20
0

Kusan mutane 31,000 ne suka nemi aikin malanta da ake son cike gurbin mutane 2,500 a jihar Osun.

Mutane 29,00 ne suka samu damar fitar da takardar zauna jarabawar neman cancantar aikin daga cikin mutane 31,000.

DCL Hausa tace kwamishinan ilmi na jihar Folorunsho Oladoyim ya sanar da hakan ga manema labarai a lokacin duba yadda zaman jarabawar ya kasance.

A watan Disambar 2020 ne gwamnatin jihar ta ayyana cewa za ta dauki karin malaman makaranta 1,500 ga makarantun sakandaren jihar, sai wasu 1,000 ga makarantun firamare na jihar a fadin jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply