Home Lafiya Mutane 313 sun daina shan taba sigari a sanadin zuwa Aikin Hajji

Mutane 313 sun daina shan taba sigari a sanadin zuwa Aikin Hajji

71
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Kamfanin Dillancin labarai na kasar Saudiyya ya ce wata kididdiga ta tabbatar da cewa alhazai 313 ne suka daina zukar taba sigari tun da aka fara aikin hajjin bana.

 

Shugaban Kamfani Dillancin labaran Abdollah Bn Dawood Al-fayez shi ne ya bayyana wa ‘yan jarida wannan tabbaci kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. bayanai sun nuna cewa alhazan sun tuba da shan sigarin ne bayan da suka ziyarci asibitocin kasar ta Saudi Arabia.

Hotan karan taba sigari

Masana harkokin kiwon lafiya dai sun ce zukar taba sigari na da illa sosai musamman ga lafiyar mutum da ke haddasa sankarar huhu.

 

Alhazai sama da Milyan 2 ne  ciki har da yan Nijeriya da sauran kasashen musulmi suka gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.

 

Ya zuwa yanzu ma, har an fara jigilar maido su gida bayan kammala aikin hajjin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply