Home Kasashen Ketare Mutane 5 sun mutu ya yin zanga-zanga a Sudan

Mutane 5 sun mutu ya yin zanga-zanga a Sudan

139
0

Mutane biyar sun rasa ransu a gabashin Sudan ya yin wata zanga-zangar nuna kin amincewa da nadin da aka yi wa Salah Ammar a matsayi sabon gwamnan jihar Kassala.

Ko a Larabar makon nan, an kashe mutum daya, kana aka jikkata karin wasu 11, kafin rikicin ya kara kamari a ranar Alhamis.

Kafofin yada labaran kasar sun bayyana cewa an cinna wa wasu manyan gine-gine wuta tare da kona shaguna ya yin zanga-zangar.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa, โ€œan kame mutane bakwai da ke da hannu a tashin hankalin,” kazalika Firai Ministan kasar Abdalla Hamdok ya aike da jami’an tsaro domin magance tashe-tashen hankulan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply