Home Labarai Mutane 500 ƴanbindiga suka raba da gidajensu a Zamfara

Mutane 500 ƴanbindiga suka raba da gidajensu a Zamfara

123
0

Aƙalla mutane 500 ne daga garuruwa 6 na ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara, ƴanbindiga suka raba da gidajensu.

Wani rahoto da BBC Hausa ta fitar a ranar Talatar nan ya ce mutanen yanzu haka suna gudun Hijira ne a garin Merere da ke jihar Kebbi, bayan ƴanbindigar sun kai hari garuruwansu tare da ƙona masu gonaki.

Kamar yadda wasu ƴan gudun Hijirar suka faɗa, da yawa daga cikin masu gudun Hijirar mata ne da yara ƙanana waɗanda ke rayuwa a wani fili kusa da maƙabarta cikin tsananin rashin abinci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply