Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Mutane dubu 333 za su amfana da tallafin ₦30,000 a Nijeriya

Mutane dubu 333 za su amfana da tallafin ₦30,000 a Nijeriya

189
0

Daga ranar daya ga watan Oktoban shekarar nan gwamnatin Nijeriya za ta ba da dama ga masu sana’o’in hannu da ma masu harkar sufurin motoci su nemi tallafin ₦30,000 domin rage masu radadin da cutar corona ga masu karamin karfi.

Karamar minista a ma’aikatar ciniki da masana’antu Maryam Yalwa Katagum ce ta sanar da hakan a Abuja lokacin da ta ke yi wa manema labarai jawabi game da shirin.

Katagum ta ce masu sana’o’in hannu da masu sufurin Motoci dubu 333 ne za su amfana da wannan tallafi na ₦30,000 a karkashin shirin tallafa wa masu kananan sana’oi.

Ta kuma ce kimanin mutane dubu 9 za su amfana da tallafin Naira milyan 270 da aka ware wa kowace jiha a karkashin shirin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply