Wasu bayanai daga hukumar zaben Nijeriya INEC sun nuna cewa mutane milyan 1.72 ne kacal suka cancanci jefa kuri’a a zaben gwamnan Edo da z a gudanar ranar Asabar din nan.
Daily Trust ta rawaito cewa a shekarar 2018, akwai wadanda suka yi rajistar zabe a jihar su milyan 2,210,534, amma dai mutane milyan 1,726,738 ne kadai suka karbi katin.
Jihar Edo dai nada kananan hukumomi 18, da mazabu 192 da kuma rumfunan zabd 2,627.
