Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Mutane milyan 21.76 na zaman kashe wando a Nijeriya

Mutane milyan 21.76 na zaman kashe wando a Nijeriya

147
0

Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta ce akwai marasa aikin yi 21,764,617 a Nijeriya.

Wannan kididdiga na kunshe ne a cikin wata manhajar hukumar da aka yi wa lakabin “rahoton rashin aikin yi” a aka fitar a Abuja.

Hukumar ta ce rashin aikin yin ya kara tsamari, ta yadda ya tashi daga kaso 23.1% zuwa kaso 27.1% a rubu’i na 3 na 2018.

Rahoton ya ce, mutane 58,527,276 ne ke da aikin yi. Sai dai rahoton ya nuna cewa an samu koma baya ga adadin kason masu aikin yin a shekarar 2020, inda ya koma kaso 15.8%

Kididdigar ta nuna cewa mutane 35,585,274 ne cikakkun ma’aikata, da ke aikin sa’o’i 40 ko fiye a mako. Sai 22,942,003 ne aikin sa’o’i 20-29 a mako.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply