Home Coronavirus Mutum 118 suka kamu da Covid-19 cikin kwana biyu a Kano

Mutum 118 suka kamu da Covid-19 cikin kwana biyu a Kano

83
0

An samu rahoton mutum 118 da suka kamu da cutar coronavirus cikin kwana biyu a jihar Kano.

Bayanai daga hukumar kula da ɓarkewar cutuka ta Nijeriya NCDC sun nuna cewa a ranar Laraba an samu mutum 38 da suka kamu da cutar a yayin da aka samu mutum 80 a ranar Alhamis.

Haka ma NCDC ta ce adadin jimillar waɗanda suka kamu da cutar ya kai 219 yayin da uku suka mutu.

Ƙaruwar yawan masu ɗauke da cutar dai ya ƙaru ne kwanaki uku, bayan an dawo da ci gaba da gwajin waɗanda ake zargi na ɗauke da cutar a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply