Home Coronavirus Mutum 350 sun warke daga cutar Covid-19 a Jamhuriyar Nijar

Mutum 350 sun warke daga cutar Covid-19 a Jamhuriyar Nijar

186
1

Sakamakon gwajin jinin da Ma’aikatar Kiwan Lafiya ta Jamhuriyar Nijarta fitar a yammacin ranar Lahadin nan na nuni da cewa adadin mutanen da suka warke daga cutar Covid-19 a yanzu a Nijar sun zarta wadanda suke fama da cutar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Dr Arba Nouhou Mukaddashin Magatakardar Ma’aikatar ta ce kawo ranar Lahadin nan cikin mutane 2712 da aka gwada jininsu daga bular cutar kawo yanzu mutum 696 ne aka tabbatar sun kamu da cutar ta Covid-19 cikin su kuma 317 ne ke ci gaba da samun kulawa daga likitoci, 350 sun warke tas yayin da wasu 29 suka hadu da ajalinsu.

Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar Mahammadu Issoufou

Daga cikin mutum 696 da ke dauke da cutar a Nijar akwai guda 12 sabbin kamu da aka fitar da sakamakon gwajinsu a ranar Lahadin nan. A cikin sabbin kamun mutum 9 na a Yamai babban birnin kasar sai mutum 3 da ke a Damagaram.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply