Home Lafiya Mutum 39,000 za su iya kamuwa da Covid-19 a Lagos kaɗai

Mutum 39,000 za su iya kamuwa da Covid-19 a Lagos kaɗai

139
0

Gwamnatin jihar Lagos ta ce akwai yiwuwar adadin waɗanda za su kamu da cutar coronavirus ya kai 39,000 a jihar.

 

 

 

Kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Akin Abayomi, wanda ya bayyana haka ga ƴan jarida a Lagos, ya ce idan har jama’a ba su rungumi tsarin bada tazara a lokacin haɗuwar su ba, to a shirya samun mutum 39,000 da za su kamu da cutar.

Saidai ya ce adadin zai iya raguwa zuwa 13,000 idan har mutane suna bin shawarwarin da ake ba su.

Ya ƙara da cewa wannan adadi na mutum 13,000 kaɗan ne idan aka yi la’akari da yadda cutar ta mamaye duniya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply