Home Labarai Mutum 7 sun mutu a haɗarin mota a Kano

Mutum 7 sun mutu a haɗarin mota a Kano

113
0

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum 7 yayinda mutum biyu suka raunata, a wani haɗarin mota da aka yi a unguwar Kunduɓawa da ke cikin birnin Kano.

Mai magana da yawun hukumar Malan Saidu Muhammad ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a ranar Laraba, a Kano.

A cewarsa haɗarin ya faru ne da asubahin ranar Laraba, lokacin da wasu tireloli biyu suka yi karo, kuma bayan an kai waɗanda haɗarin ya rutsa da su a asibitin Sir Sunusi aka tabbatar da mutum 7 sun mutu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply