Home Labarai Mutum 8 sun kamu da Lassa a Kaduna, 2 sun warke 4...

Mutum 8 sun kamu da Lassa a Kaduna, 2 sun warke 4 sun mutu

86
0

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna ta ce ta samu nasarar warkar da mutum biyu daga cikin mutane 8 da aka tabbatar sun kamu da zazzabin Lassa a jihar.

Gwamnatin ta kuma ce ana ci gaba da kula da wani dan shekara 40 da aka tabbatar yana dauke da cutar a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Kwamishinar lafiya ta jihar Dr Amina Muhammad Baloni ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Asabar, tana mai cewa mutum hudu daga cikin wadanda suka kamu da cutar sun mutu.

Ta yi bayanin cewa mutum 8 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar daga cikin mutum 74 aka yi zargin suna dauke da cutar daga ranar 22 ga watan Janairu.

Kwamishinar ta bayyana bukatar da ke akwai na mutane su kai rahoton duk wanda ya nuna alamun kamuwa da cutar don daukar mataki cikin lokaci.

Ta kuma shawarci jama’a da su rika tabbatar da tsabtar jiki da ta muhallan su, domin kaucewa kamuwa da cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply