Home Lafiya Mutum na farko da ake zargi ya kamu da coronavirus a Katsina

Mutum na farko da ake zargi ya kamu da coronavirus a Katsina

73
0

Ma’aikatar lafiya ta jihar Katsina ta sanar da samun mutum na farko da ake zargin ya kamu da cutar coronavirus a jihar.

Da yake yiwa ‘yan jarida bayani da safiyar yau Laraba, babban sakatare a ma’aikatar Lafiyar Dr Kabir Mustapha, ya ce mara lafiyar, wanda yanzu haka aka kebance shi, bai jima da dawowa daga Malaysia ba, inda ya rika nuna wasu alamu da ke bukatar bincike na musamman.

Ya kuma yi bayanin cewa ma’aikatar na daukar dukkan matakan da suka dace, kuma tana aiki tare da cibiyar kula da barkewar cutuka ta Nijeriya kan wannan batu.

Babban sakataren ya yi kira ga jama’ar Dutsinma, garin da mara lafiyar ya fito, da su zama masu taka tsantsan a hada-hadar da suke yi da kuma shiga taron mutane.

Ya kara da cewa, jama’a kar su yi shakkun neman magani a asibiti, domin kuwa an dauki dukkan matakan da suka da ce don tallafawa jama’a.

Yawan wadanda suka kamu da wannan cuta dai ya kai mutum uku bayan da ma’aikatar lafiya ta tabbatar da mutum na uku da ya kamu da cutar a Enugu.

Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ya bayyana cewa wadda ta kamu da cutar ‘yar Nijeriya mai shekaru 30 da ta dawo daga Birtaniya a ranar 13 ga watan Maris bayan wata guntuwar ziyara da ta je.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply