Home Labarai Mutum uku sun mutu a haɗarin motar tawagar Zulum

Mutum uku sun mutu a haɗarin motar tawagar Zulum

33
0

‘Yan siyasa uku ne suka mutu a wani hatsarin mota da tawagar Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ta yi, kan hanyarsu ta dawowa daga Mafa, maihafar gwamnan.

Gwamnan ya dawo ne daga kauyensa a ranar Talatar nan, bayan ya kaddamar da sabunta katin rajistarsa na jam’iyyar APC.

Wadanda ke cikin tawagar gwamnan sun hada da tsohon gwamnan jihar Kashim Shettima, Shugaban riko na jam’iyyar APC a jihar, Kakakin Majalisar Dokokin jihar da sauran ‘yan jam’iyyar da dama.

Shaidun gani da ido sun ce tayar motar ce ta fita inda ta fara tsalle a titi, kuma ta yi silar mutuwar mutum uku da ke cikin motar da suka hada da shugaban kungiyar Kabilar Kanuri da ke jihar Lagos, Mai Masa Mohammed.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply