Home Labarai Mutumin da ya kashe matarsa da dansa

Mutumin da ya kashe matarsa da dansa

32
0

Rahotanni daga jihar Anambra sun ce wani magidanci mai suna Chukwuemeka Obijofa na kauyen Ofufe Nza a karamar hukumar Ekwusigo ta jihar ya kashe matarsa da dansa da sheburi.

Wata majiya daga yankin tace kwatsam an ga Obijofa ya dankara da gudu inda ya tarar da matarsa mai shekaru 26 Chisom da danta mai shekaru 4 inda ya yi ta buga musu shebur a kai.

Majiyar ta kuma ce mutumin ya kuma sanya wannan sheburi da ya yi aika-aikar, ya kuma buge dan sintirin da ya yi yunkurin kai dauki.

Rundunar ‘yansandan jihar ta Anambra ta hannun mai magana da yawunta CSP Haruna Mohammed ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply