Home Labarai Mutuwar matashi ofishin Ƴan sanda: An ƙaddamar da kwamitin bincike a Kano

Mutuwar matashi ofishin Ƴan sanda: An ƙaddamar da kwamitin bincike a Kano

166
0

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta ce ta kafa kwamitin bincike kan zargin kisan wani matashi ɗan shekara 17, Saifullahi Sani-Musa a ofishin ƴan sanda.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna ya fitar, ya musanta cewa ƴan sanda suka kashe shi, yana mai cewa an kafa kwamitin binciken lamarin.

A cewarsa jami’an kiwon lafiya sun tabbatar da mutuwar matashin, yayin da ake ci gaba da binciken musabbabin mutuwarsa, kuma an jibge jami’an tsaro a yankin don tabbatar da doka da oda.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply