Home Labarai Naɗin hafsoshin tsaro: Buhari na neman amincewar majalisa daga baya

Naɗin hafsoshin tsaro: Buhari na neman amincewar majalisa daga baya

48
0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rubuta wa majalisar Dattawan Nijeriya yama neman ta tabbatar masa da naɗin da ya yi na sabbin hafsoshin tsaron ƙasar.

A takardar da Buhari ya aikewa shugaban majalisar Ahmed Lawan ɗauke da kwanan watan 27 ga Janairun 2021, ya ce neman amincewar majalisar na a ƙarƙashin dokokin rundunar sojin Nijeriya.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa Shugaban ƙasar a ɓangaren majalisar dattawa Sanata Babajide Omoworare ya fitar a ranar Juma’a.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply