Home Sabon Labari Na haramta wa kaina sake neman shugabancin APC – Oshiomhole

Na haramta wa kaina sake neman shugabancin APC – Oshiomhole

101
0

Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya ce ba shi da niyyar sake neman shugabancin jam’iyyar, wadda ya shugabanta na tsawon shekaru biyu.

A cikin wata sanarwa da shi kansa ya fitar a ranar Litinin, tsohon shugaban na APC, ya jaddada cewa ba zai taba sake neman shugabancin ba ko da kuwa an yi masa tayin hakan.

A cewarsa, ko da majalisar zartaswar jam’iyyar ko hukuncin kotu ya umarce shi ya sake dawowa shugabancin jam’iyyar ba zai taba dawowa ba.

Oshimole ya yi bayanin cewa ya bayyana matsayar tasa ce, biyo bayan karar da wani daga cikin ‘yan rusasshen kwamitin shugabancin jam’iyyar ya shigar.

Duk da yake bai bayyana ko waye ya dauki wannan matakin ba, saidai ya koka a kan yadda dan siyasar ya ce shi magoyin bayansa ne.

Adams Oshiomhole ya kuma bayyana irin rawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka wajen ganin ya zama shugaban jam’iyyar a watan Yunin shekara ta 2018, yana mai cewa har yanzu shi mai biyayya ne ga gwamnatin Buhari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply