Home Coronavirus NAFDAC na gwajin magungunan corona da ta samu daga masu magungunan gargajiya

NAFDAC na gwajin magungunan corona da ta samu daga masu magungunan gargajiya

171
0

Hukumar kula da ingancin abinci da kuma magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta ce tana ci gaba da yin bincike tare da yin nazari dama duba ingancin magungunan gargajiya da ta samu kusan kala 20 da masu maganin gargajiya suka kawo mata.

Farfesa Mojisola Adeyeye ita ce ke Shugabantar hukumar ta NAFDAC ta bayyana haka a wani zama na musamman da ta yi da kwamitin yaki da cutar corona na majalisar wakilan kasar nan.

Mojisola ta kara da cewa hukumar za ta bayyana tare da sabunta sakamakon binciken nata da zarar ta kammala.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply