Home Labarai NAFDAC ta gargaɗi masu shan lemun kwali

NAFDAC ta gargaɗi masu shan lemun kwali

193
0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta yi gargaɗi jama’a su guji shan lemun kwali na ƴan ƴan itacen tuffa da baƙin inabi da ake shigo da su daga ƙasar Austiraliya.

Shugabar hukumar Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ta bayyana cewa lemun na da illa ga lafiyar al’umma domin suna ɗauke da sinadarin Patulin wanda ka iya haifar da ciwon koɗa da hanta a jikin ɗan adam.

Mujisola ta buƙaci ƴan kasuwar da ke shigo da irin waɗannan nau’in lemu da su dakatar da shigowa da su, sannan ta yi kira ga ƴan ƙasar da ke amfani da su, su dakatar da shan su domin inganta lafiyarsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply