Home Labarai NAFDAC ta rufe kamfanonin haɗa magunguna

NAFDAC ta rufe kamfanonin haɗa magunguna

108
0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta rufe kamfanonin haɗa magunguna shida, saboda rashin bin ƙa’idar inganta aiki.

Babbar Daraktar Hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta faɗi haka a cikin wata sanarwa da Sayo Akintola jami’in yaɗa labaran hukumar ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Adeyeye ta ce matakin na daidai da ƙoƙarin hukumar na hana yaɗuwar jabun magunguna da marasa inganci a ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply