Home Labarai Nafi karfin sojojin Nijeriya – inji Shekau

Nafi karfin sojojin Nijeriya – inji Shekau

310
0
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya sake caccakar babban kwamandan sojojin Nijeriya a cikin wani sabon faifan bidiyo da ya fitar, inda ya ce ba za su iya kama shi ba saboda yana yin aikin Allah ne, kamar yadda jaridar Tribune ta bayyana.

Shugaban rundunar sojan kasar nan, Janar Tukur Buratai ya sha umartar jami’ansa da su kama Shekau din.

Ko kafin a zabe shi Shugabancin Nijeriya, shugaba Muhammadu Buhari a lokutan yakin neman zabensa ya sha bayyana cewa cewa zai murkushe kungiyar Boko Haram cikin kankanin lokaci idan ya hau mulki.

A sabon bidiyon, mai tsawon Mintuna 30, Shekau ya ce babu yadda za a yi a iya kama shi, domin aikin Allah yake yi kuma shi ne zai kare shi da sauran kwamnadojin yaƙinsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply