Hukumar alhazai ta Nijeriya NAHCON, ta sanar da amincewa ga kamfanonin jiragen sama guda biyar da za su yi jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa aikin Hajjin 2027.
NAHCON ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce an zaɓi kamfanonin ne bayan wani cikakken tsarin tantancewa da hukumar tantance kamfanonin jiragen sama ta gudanar.
Sanarwar ta ce an yi tantancewar ne bisa la’akari da ƙa’idojin tsaron jiragen sama, ƙwarewar gudanar da ayyuka da kuma ƙarfin kuɗi na kamfanonin.
Kamfanonin jiragen saman da gwamnati ta amince da su sun haɗa da Air Peace Limited, Flynas, Max Air Limited, Saudi Air da UMZA Aviation Services Limited.
Sai dai NAHCON ta ce amincewar tana ƙarƙashin sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazai da hukumar, da kuma cika dukkan buƙatun hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Saudiyya (GACA).
Hukumar ta ce za a tsara adadin maniyyatan da kowane kamfani zai ɗauka da kuma jadawalin tashin jiragen ne tare da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da kamfanonin jiragen saman.
NAHCON ta kuma ce dukkan kamfanonin da aka amince da su dole ne su bi ƙa’idojin aikin Hajjin 2027, ciki har da samar da tikitin jirgi da ke da alaƙa da bayanan maniyyata na Nusuk-Masar.
Haka kuma, kamfanonin za su tabbatar da bin dukkan ƙa’idojin tsaro da aka gindaya, tare da kiyaye dokokin kayan da kowane mahajjaci zai iya tafiya da su.
A cewar hukumar, kowane mahajjaci zai samu damar tafiya da akwatin kaya guda mai nauyin kilo 32 da kuma ƙaramin kaya na hannu mai nauyin kilo 8, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka tanada.
NAHCON ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki, musamman hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da maniyyata, da su ba kamfanonin da aka amince da su cikakken haɗin kai domin tabbatar da jigilar alhazai cikin sauƙi, tsaro da kwanciyar hankali.
