Home Addini NAHCON ta bayyana yawan kudin kujerar aikin Hajjin 2020 na Katsina.

NAHCON ta bayyana yawan kudin kujerar aikin Hajjin 2020 na Katsina.

96
0

Abdullahi Garba Jani

A ranar Litinin 18 ga wannan wata na Nuwamba, 2019 ne hukumar kula da alhazai ta jihar Katsina za ta fara rajista tare da amsar kudin ajiya na aikin hajjin 2020.

Mukaddashin daraktan hukumar Malam Dalhat Usman ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke karin haske ga manema labarai kan shirye-shiryen aikin hajjin 2020 a Katsina.

Malam Dalhat Usman ya ce sanar da fara amsar kudin ajiyar ya samo asali ne bayan da gwamna Aminu Masari ya amince bayan da hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta umurta.

Ya ce ana kyautata zaton maniyyatan za su biya milyan daya da rabi (1.5) ko kuma su rika zuba Naira dubu dari uku-uku duk wata har su biya daga Litinin zuwa watan Maris na 2020.

Sai ya ja kunnen maniyyata aikin Hajjin da cewa ta yardajjen bankin ne kadai za su zuba kudadensu ga hukumar kula da aikin hajjin.

Har ma ya ce hukumar ba ta amsar kudi hannu da hannu, sai dai ta banki,, don kuwa a ta bakinsa, duk wanda ya yi haka, to don kanshi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply