Hukumar Imagireshin: NAJERIYA TA SAMU NAIRA BILYAN 20 DAGA YAN KASASHEN WAJE MASU ZAMA NAJERIYA.
Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta bayyana a yau Lahadi cewa Najeriya ta samu kudin lasisin da take karba daga yan kasashen waje har Naira Bilyan 20.5. NBS tace a tarihin Najeriya, hukumar shige da fici ba ta taba tara irin wannan kudi masu yawa haka ba a wannan bangaren.
A ganinku me ya kamata gwamnati tayi don kara inganta aikin Imagireshin ?
