Home Sabon Labari Najeriya ta sake rage farashin fetur

Najeriya ta sake rage farashin fetur

578
0

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya sanar a ranar Laraba cewa ya rage farashin kudin litar fetur da yake sayarwa masu gidajen mai. Rage farashin ya kai na kaso 17.94 a cikin dari.

Kafin sanarwar ta ranar Laraba dai gwamnati na sayar wa ‘yan kasuwa litar fetur a kan Naira 108 su kuma sai su dora ribarsu a karkashin amincewar hukumar kayyade farashin fetur ta PPPRA.

A yanzu tun da an samu sabon ragi na kaso 17.94 ana dakon hukumar PPPRA ta sanar da ragin a hukumance ta yadda ‘yan Najeriya za su fara biyan kasa da kudin da suke sayen fetur a halin yanzu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply