Home Labarai Nan ba da jimawa ba ASUU za ta janye yajin aiki –...

Nan ba da jimawa ba ASUU za ta janye yajin aiki – Ngige

181
0

Ministan kwadago da ingantuwar aiki, Dr. Chris Ngige, ya ce nan ba da dadewa ba kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU za ta dakatar da yajin aikin da take yi.

Ngige ya yi wannan bayanin ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels cikin shirinsu na turanci mai suna Politics Today” wanda aka watsa da yammacin Talatar makon nan.

Ya yi bayanin cewa, Ma’aikatar Kudi, Ilimi, Kwadago da kuma ofishin babban akanta janar na kasa za su hadu da kungiyar domin a sasanta matsalolin da kungiyar ta ASUU ke korafi kan su, musamman ma salon biyan albashi na bai daya da gwamnatin ta bijiro da shi wato IPPIS.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply