Home Noma da Kiwo Nan ba da jimawa ba farashin shinkafa zai daidaita-Gwamna Bagudu

Nan ba da jimawa ba farashin shinkafa zai daidaita-Gwamna Bagudu

78
0

Abdullahi Garba Jani

Gwaman jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ce irin yabanyar da aka samu a daminar bana zai taimaka wajen daidaita farashin shinkafa a kasuwannin Nijeriya.

Atiku Bagudu da ke jagorantar kwamitin shugaban kasa na inganta noman shinkafa ya yi wannan furucin ne a Argungu lokacin da ya ke ganawa da manoman yankin.

Ya ce yabanyar da aka samu za ta sa rage yawan shigo da shinkafar waje, a rika amfani da ta gida don noman ya ci gaba da inganta.

Gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba, gwamnati za ta samar da injinan casar shinkafa ta rarraba ga manoma don inganta sarrafa ta.

Daya daga cikin manoman, Abubakar Usman ya fada wa gwamna Bagudu cewa sun samu yabanya mai kyau a daminar bana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply