Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, ya ce Nijeriya na iya samun allurar rigakafin COVID-19 a cikin kwanaki 10 masu zuwa.
Osagie ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, ga manema labarai a yayin ziyarar duba asibitin koyarwa na jami’ar Legas, Idi-Araba.
Ya ce “An gaya mana cewa a karshen wannan watan, wanda yake shi ne kimanin kwanaki 10 daga yanzu, za mu sami allurar.
“Ba mu ke samar da allurar ba, an samar da su ne a ƙasashen waje a cikin ƙasashe kusan huɗu ko biyar ” inji shi.
