Daga Rahama Ibrahim Turare.
Gwamnan jihar Ekiti Dr. Kayode Fayemi, ya ba da tabbacin cewa Nijeriya za ta fita daga kangin talaucin da take fama da shi nan da shekara ta 2030.

Gwamnan ya ce haka zai yiwu idan aka bi yadda aka tsara acikin shirin nan mai taken ci gaba mai dorewa (Sustainable Development Goals policy).

Fayemi ya karfafa wa matasan Nijeriya gwiwa da su gina kansu da kansu ta hanyar basira da hikima da Allah ya basu ta yadda za su yi kunnen-doki da sauran takwarorinsu na kasashen duniya.
Ya kara da cewa makasudin wannan shirin na SDGs shi ne domin yakar talauci da fatara a duniya baki daya ta yadda duniyar za ta yi dadin zama ga kowa da kowa nan da shekara ta 2030.
