Home Sabon Labari Nasarawa ta haye teburin Firimiyar Nijeriya bayan wasa na 6

Nasarawa ta haye teburin Firimiyar Nijeriya bayan wasa na 6

26
0

Bayan samun nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Warri Wolves da ci 2-1 Nasarawa United ta samu damar darewa teburin gasar firimiyar Nijeriya.

Damar jefa kwallon da Ohanachom ya samu ne ya taimaki kungiyar ta Nasarawa yin nasara a wasa 4, inda suka yi kunnen doki a wasa 2 cikin wasa 6 da suka buga.

A filin wasan Godswill Akpabio kuwa Sunshine Stars ce ta doke Dakkada da ci 2-1 wanda hakan ya ba su damar matsawa zuwa na 6 a gasar.

Kwara United kuwa ta yi nasara akan bakuwar tasu IfeanyuUbah da ci 1-0 a filin wasansu na Kwara dake garin Illorin.

Heartland ta lakume Akwa United da ci 2-1 a filin wasansu na Dan Anyiam a garin Owerri.

MFM sun tashi kunnen doki 0-0 da Abia Warriors, wanda hakan ya jefa makomar shugaban kungiyar ta Warriors Imama Amapakabo cikin rudani tun bayan da suka bashi lamunin wasa 3 anan gaba, kasancewar haryanzu Warriors ba su yi nasara ba adukkanin wasa 6 da suka buga.

Haka Enugu Rangers ma sun tashi kowa na neman sa’a 0-0 a wasansu da Lobi Stars da suka buga a filin wasa na Nnamdi Azikiwe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply